Skip to main content

YADDA ZAKA KARE ACCOUNT DINKA NA FACEBOOK DAGA BLOCKING KO HACKING.

Assalamu Alaikum,
to cikin ikon Allah yau zamu tattauna ne akan wancan take da na bayar a sama, inda zan kawokadan daga abubuwan da ya kamata mu sani kuma mu kiyaye game da account din mu, sai a biyo mu.
1.Yana da kyau ka dinga canja password din ka akalla bayan sati daya (1) zuwa sati biyu,
sannan wajen canjawar a guji sanya 123456 ko sunan ka, ko kuma lambar wayarka, sunan budurwar ka, ko unguwar ka, a’a yana da kyau ka sanya harufa da kuma lambobi, kai harma da symbols kamar @”-+, sannan kada ka yarda ka sanar da wani wannan password din naka.
Sannan a kula kada kayi amfani da password guda daya a dukkan abubuwanka misali a Email dinka da kuma facebook din ka da sauran abinda kake budewa duk su zama iri daya domin hakan zai baiwa wasu damar yin awon gaba da account dinka.
2. Sanya Karin email akan account dinka a kalla ina bada shawarar kayi adding email kamar guda uku (3) akan account dinka kaga kana da cikakken iko akan account dinka duk wani motsi ko wani yunkuri da akayi kai tsaye zaka gani.
Sannan a setting na email din ka mayar dashi babu wanda zai iya ganin su sai kai kadai “only me” a yaren facebook,
3. Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki kana samun sakonni acikin ta da yawan mu lambobin da muka bude facebook dasu mun rasa layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar daga kan fb din mu canza ta da lambar da muke da ita a yanzu, rashin yin hakan zai bamu matsala don haka idan kasan ka rasa layin ka to ka canza lambar layin ka na yanzu domin ka cigaba da samun sakonnin facebook.
4. Ka sanya“Login Approval”a account din ka yadda zaka sanya shine ka bi wannan hanyar kaje :Home -> Account Settings -> Security ->Login Notification sai ka mai da shi “Enable”
Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na account din ka sannan idan zakayi login dole sai an turo maka da code ko kuma kayi approving ta wayarka idan android ce, sannan anan bangaren zaka iya samar da“code generator” ta yadda zaka samar da wani code wanda kai ka dai ne ka sanshi idan kazo yin login bayan password to shi ma zaka saka shi.
5. Sannan zaka iya zabar wasu amintattu daga friend dinka kamar Guarantor kenan ka sanya su,
suma zasu iya baiwa account din ka kariya.
6. Ka samar da tsayayyiyar browser da kake hawa facebook,
kada ka zama yau ka ari wayar wancan ka hau gobe ka ari ta wancan, sannan a daina yin saving din password a browser saboda zaka iya yadda wayar ka, ko kuma a dauke maka ita, mu samman a wannan lokacin da ake yawan kwace kaga wani zai iya hawa,
sannan facebook zasu iya yi maka blocking saboda yawan yin hakan.
7. Ka dinga yin log out duk sanda ka hau idan zaka sauka.
8. Kada ka baiwa wani ko wata bayanan ka na yin login a account din ka ko wani web site.
1.Kayi tunani kafin ka danna link, zaka ga ance ka danna link, to ka fara yin tunani kafin ka shiga,
misali ace ka danna kaga abinda zai faru ko makamantan hakan, ko idan ka shiga sai kaga ance ka saka password dinka to duk irin wannan sai a kiyaye.
2. Kayi login a www.facebook.com ka wai www.fb.com kada kayi login a facebook ta kan wani site daban ba wannan ba, ko application wanda ba ingantacce ba.
3. Ka dinga yin updating din browser din ka ko application din ka.
4. ka dina installing anti virus a wayar ka ko a computer da kake amfani da ita.
5. ka daina yawan tura Requesting ko yawan yin accepting ka kula wajen karbar wanda baka san shi ba, yana da kyau ka duba propile din sa kafin kayi accepting din sa.
6. Ka daina yawan yin sharing na wani link da baka tantance shi ba.
7. ka daina hade facebook account dinka da ko wane shafukan internet, zaka ga da yawa daga website ana yin register din su ta facebook mai makon kayi da email sai kayi da facebook shima wannan ya kamata ayi tunani sosai kafin aiwatarwa.
8. Kada ka yi wani posting wanda ya sabawa wadansu to idan suka yi ta yin reporting din Ka a facebook su ma zasu yi blockin din account din ka.
Bara na dakata anan naga rubutun zaiyi tsayi da yawa.

NAKU RABIU MUSA

© Basheer Sharfadi

Comments

Popular posts from this blog

SUJJADAR QABLI DA BA'ADI.

Yadda ake yin SUJJADAR QABLI da SUJJADAR BA’ADI 1. Sujjada Qabli : ana yinta ne kafin sallama. Bayan mutum yayi tahiya, kafin yayi sallama, sai ya sake yin wasu sujjudu guda biyu, sannan ya sake yin wata tahiyar, Sannan yayi sallama. Wannan ita ce Sujjadar Qabaliy, Dalilan da suke sawa ayi ta: Idan mutum yayi ragi a cikin Sallarsa, Ko kuma ya tauye wasu sunnoni Qarfafa guda biyu ko sama da haka. (a takaice kenan). 2. SUJJADA BA’ADI : ana yinta ne duk yayin da aka Qara wani abu acikin Sallah. Kokuma yayin da mutum ya mance da wata farillah, ko kuma rukuni daga cikin sallar sa. Bayan ya kawo wannan farillar da ya mance, to sai yayi sujjadar Ba’adi. YADDA AKE YINTA : Ana yinta ne bayan anyi tahiya anyi sallama, sai a sake yin wasu sujjudu guda biyu, sannan ayi tahiya ayi sallama. ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ : ﻓَﻤَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﻏَﻴْﺮَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺓِ ﺍْﻹِﺣْﺮَﺍﻡِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺳَﻤ...

BAZAI AUREKI BA WANCAN!!

BAZAI AUREKI BA WANCAN!! Daga malama Aisha isah. Wannan dayake tambayar kalan kayanki da daddare bazai aureki ba❗️ Da wannan dayake so kitura mai hotonki bayan kinyi shirin bacci❗️ Haka dai wannan dayake so yayi magana dake da daddare akan magana na rashin kama kai da karancin kunya, shima bazai aureki ba‼️ Hakama wannan daya tareki ahanya da maganar banza, kuma yanemi lambar wayarki shima bazai aureki ba❗️ Hakama wannan dayake daukanki a sabuwar moto, yana yawo dake, yana sai maki abubuwan ci masu dadi shima bazai aureki ba❗️ Wancan shima dayake bada labarinki acikin abokansa suna miki dariya, bazai aureki ba❗️ Wannan ma dayake ta wasa da hankalinki da zuciyarki shima bazai aureki ba❗️ DAN TSAYA KIJI    ✋ Wannan dayazo neman aurenki da zuciya daya, kuma yaboye kololuwar soyayyar dayake miki har zuwa Daren ranar aurenku sannan yabaki labarinta, wannan shine Wanda dama zai aureki kuma masoyi na gaskiya. Allah ya datar da yayan musulmi da abokan zama nagar...

RAMADAN: YADDA AKE FIDDA ZAKKAN FIDDA KAI (KONO) DA HUKUNCE-HUKUNCEN TA.

RAMADAN: Yadda ake fidda zakkan fidda Kai (Kono) da hukunce-hukuncen ta.  Daga Imam Bello Mai-Iyali BY PREMIUM TIMES Godiya tatabbata ga Allah mai Girma da daukaka, Mai kamala a cikin sunayensa, wanda ya siffantu da siffofi na daukaka, Ubangijin sammai da kassai, Na shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shida abokin tarayya, ma-abucin falala da bata karewa. Na shaida Annabi Muhammad (SAW) bawansa ne kuma manzonsa ne, Ya Allah ya kara tsira da aminci agareshi da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka! Bayin Allah, Kuji tsoron Allah, kusani lallai annabinku ya wajabta muku Zakkar Fidda Kai, don ta gyara zuciya kuma ta tsarkake ta, Allah SWT ya ce “Hakika wanda ya tsarkata (zuciya) ya samu babban rabo” Zakkar Fidda Kai sadaka ce ta wajibi akan kowane Musulmi mai ikon fitarwa. Ana fitar da Zakkar Fidda Kai ne kafin Sallar Idi, tsarki ne ga mai azumi kuma abinci ne ga talaka, Sahabi Abbadullahi Dan Abbas, Allah ya yarda da shi ya ce, man...