BAZAI AUREKI BA WANCAN!! Daga malama Aisha isah. Wannan dayake tambayar kalan kayanki da daddare bazai aureki ba❗️ Da wannan dayake so kitura mai hotonki bayan kinyi shirin bacci❗️ Haka dai wannan dayake so yayi magana dake da daddare akan magana na rashin kama kai da karancin kunya, shima bazai aureki ba‼️ Hakama wannan daya tareki ahanya da maganar banza, kuma yanemi lambar wayarki shima bazai aureki ba❗️ Hakama wannan dayake daukanki a sabuwar moto, yana yawo dake, yana sai maki abubuwan ci masu dadi shima bazai aureki ba❗️ Wancan shima dayake bada labarinki acikin abokansa suna miki dariya, bazai aureki ba❗️ Wannan ma dayake ta wasa da hankalinki da zuciyarki shima bazai aureki ba❗️ DAN TSAYA KIJI ✋ Wannan dayazo neman aurenki da zuciya daya, kuma yaboye kololuwar soyayyar dayake miki har zuwa Daren ranar aurenku sannan yabaki labarinta, wannan shine Wanda dama zai aureki kuma masoyi na gaskiya. Allah ya datar da yayan musulmi da abokan zama nagar...
RAMADAN: Yadda ake fidda zakkan fidda Kai (Kono) da hukunce-hukuncen ta. Daga Imam Bello Mai-Iyali BY PREMIUM TIMES Godiya tatabbata ga Allah mai Girma da daukaka, Mai kamala a cikin sunayensa, wanda ya siffantu da siffofi na daukaka, Ubangijin sammai da kassai, Na shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shida abokin tarayya, ma-abucin falala da bata karewa. Na shaida Annabi Muhammad (SAW) bawansa ne kuma manzonsa ne, Ya Allah ya kara tsira da aminci agareshi da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka! Bayin Allah, Kuji tsoron Allah, kusani lallai annabinku ya wajabta muku Zakkar Fidda Kai, don ta gyara zuciya kuma ta tsarkake ta, Allah SWT ya ce “Hakika wanda ya tsarkata (zuciya) ya samu babban rabo” Zakkar Fidda Kai sadaka ce ta wajibi akan kowane Musulmi mai ikon fitarwa. Ana fitar da Zakkar Fidda Kai ne kafin Sallar Idi, tsarki ne ga mai azumi kuma abinci ne ga talaka, Sahabi Abbadullahi Dan Abbas, Allah ya yarda da shi ya ce, man...