RAMADAN: Yadda ake fidda zakkan fidda Kai (Kono) da hukunce-hukuncen ta. Daga Imam Bello Mai-Iyali BY PREMIUM TIMES Godiya tatabbata ga Allah mai Girma da daukaka, Mai kamala a cikin sunayensa, wanda ya siffantu da siffofi na daukaka, Ubangijin sammai da kassai, Na shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shida abokin tarayya, ma-abucin falala da bata karewa. Na shaida Annabi Muhammad (SAW) bawansa ne kuma manzonsa ne, Ya Allah ya kara tsira da aminci agareshi da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka! Bayin Allah, Kuji tsoron Allah, kusani lallai annabinku ya wajabta muku Zakkar Fidda Kai, don ta gyara zuciya kuma ta tsarkake ta, Allah SWT ya ce “Hakika wanda ya tsarkata (zuciya) ya samu babban rabo” Zakkar Fidda Kai sadaka ce ta wajibi akan kowane Musulmi mai ikon fitarwa. Ana fitar da Zakkar Fidda Kai ne kafin Sallar Idi, tsarki ne ga mai azumi kuma abinci ne ga talaka, Sahabi Abbadullahi Dan Abbas, Allah ya yarda da shi ya ce, man...