Assalamu alaikum yan uwa barkanku da wannan lokaci da zan zayyano maku yadda zakayi download daga facebook dinka Daga Dan uwanku Rabiu Musa mai shafin Duniyar Fasaha yake tare daku.
Ba tare da bata lokaci ba zan fara bayani dalla dalla ta yanda zaka sauke wannan video daga facebook dinka, sau da yawa zaka ga mutum yaci karo da video a facebook yana bukatar sa amma ba yadda ya iya dole sai dai ya wuce shi to ga bayani nan saika bi domin saukeshi kai tsaye.
1- abu na farko ka tabbatar kana da opera a wayarka idan babu to sai ka tanada, bayan ka mallaki opera dinka to kaje kan ta kayi login facebook account dinka akanta.
2- duk lokacin da kake kan facebook account dinka ko Facebook App ko Facebook lite da zarar kaci karo da video da kake san saukewa a wayarka abunda zakayi shine kayi sharing din shi wannan video zuwa timeline naka, bayan kayi shared dinsa saika sauka kaje kan opera dinka ka hau ka nufi timeline kai tsaye kana zuwa zaka ga wannan video naka da kayi shared saika danna kan video zaka ga ya nuna maka download shikenan saika danna ka sauke abunka.
3- wannan hanyar ita kuma duk lokacin da kaci karo da video a Facebook App To Abinda zakayi shine akwai wani guri da zaka ga tsage tsage kuda 3 zuwa hudu a jikin posting din saika danna gurin zaka ga ya baka rubutu zabi da yawa to saika duba inda aka sa save ka danna domin kayi save din video, bayan kayi save din saika koma kan opera dinka ka hau Facebook dinka daga sama gurin chat, notification zaka ga wani guri an sa menu to nan zaka shiga bayan ka shiga saika yo kasa zakaga saved to anan video dinka yake dakayi save daga Facebook App dinka saika taba gurin zai kaika gurin da video yake saika taba view post zai nuna maka video ma dakayi saved saika taba domin saukewa.
4-. Ko kuma Ka kofa link na bidiyon sai ka festin din shi a video downloader dake kan kwamfuta ko wayar Ka nan take zai baka daman saukewa sai ka sauke shi.
Wannan shine takaitaccen bayani akan yadda zaka sauke video daga facebook.
NAKU RABIU MUSA

Comments
Post a Comment